November 30, 2021

Harin gidan yari a Jos: Mutane 11 sun hallaka, fursunoni 252 sun tsere

Daga Danjuma Makery


An kai hari kan jami’an tsaro na hukumar gyaran hali da ke tsare wata gidan gyaran hali a jihar Jos.

Rahoto ya nuna cewa fursunoni 9 hade da wani jami’in hukumar gyara hali ne suka rasa rayukan su a yayin harin.

Mai magana da yawun hukumar ta “NCoS” a jihar Filato, Geoffrey Longdiem a yayin da yake hira da manema labarai a jiya Litinin, ya bayyana cewa daya daga cikin maharan ya rasa ransa a yayin musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

Ya kuma ce, fursunoni kimanin 252 Wanda ke tsare a gidan gyaran halin sun tsere a yayin harin.

Ya zuwa lokacin da aka kai harin, jumullan fursunonin da ke tsare a gidan gyaran halin su kai mutane 1,060 wanda suka hada da mutane 560 wadanda ke jiran shari’a.

Kwamanda Janar na hukumar, Haliru Nababa ya jajanta wa iyalai da abokan jami’in da ya rasa ransa a yayin gumurzun.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Harin gidan yari a Jos: Mutane 11 sun hallaka, fursunoni 252 sun tsere”