December 1, 2021

Harin gidan yari a Jos: Dalilan da suka haifar da nasarar ‘yan bindiga

Mujtaba Hamza Koki


Mataimakin shugaban hukumar gyaran hali, Ahmed Tukur ya bayyana dalilin da yasa yan bindigan suka yi nasara a harin da suka kai gidan yarin Jos, inda ya bayyana daya daga cikin dalilan na kasantuwar jami’an tsaro dake rike da makamai a tare da su lokacin harin sun karamta.

A yayin kai harin, ‘yan bindigan sun saki fursunoni kimanin 252 Wanda kuma dukka sun tsere.

Mataimakin shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a yayin da ya ziyarci gidan yarin da lamarin ya faru jiya Talata, inda yace adadin ‘yan bindigan da suka zo don gudanar da harin sun ninka adadin jami’an da ke tsare da wurin don haka suka samu damar kutsawa cikin gidan yarin.

A ganawar da yayi da ‘yan jaridu yayin ziyarar, mataimakin shugaban hukumar ya ce “… a yayin da yan bindigan suka iso wurin sun iske jami’an mu a wurin, inda suka bude musu wuta a mashiga”.

Ya kuma cigaba da cewa “sun kashe daya daga mutane na, kana suka shiga cikin wurin da karfin tsiya inda suka saki wasu fursunoni”.

Inda yace “ka yi tunanin inda fursunoni suma da 200 ke kokarin tserewa, a bangare guda kuma ga adadin ‘yan bindigan da suka kawo harin, shin zaka iya gwada adadin su da adadin jami’an mu da ke tsare da wurin a wannan lokacin?”

“Adadin fursinonin bazai yiwu a kwatanta shi da na jami’an mu da ke bakin aiki a lokacin ba.

“Sai dai kuma hakan ba Yana nufin cewa jami’an mu sun zuba ido ko gajiya wurin mayar da martani ba, a yayin musayar wuta tsakanin su day maharan ne har wasu fursunoni da ke kokarin guduwa suka raunata saboda harbin bindiga, a bangare guda kuwa daya daga maharan ya rasa ransa.

A karshe ya bayyana cewa tuni sun fara gudanar da bincike kan lamarin.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Harin gidan yari a Jos: Dalilan da suka haifar da nasarar ‘yan bindiga”