April 13, 2023

Hare-haren ’yan bindiga ya yi sanadin mutuwar mutane 134 a Nijeriya

Mutane a kalla 134 ne suka rasa rayukansu cikin kwanaki 5, sanadiyyar wasu mabanbantan hare-hare da ’yan bindiga suka kai jihar Benue, dake yankin tsakiyar Nijeriya.

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya shaidawa manema labarai a Makurdi babban birnin jihar cewa, an kai hare-haren ne kauyuka dake yankunan kananan hukumomin Otukpo da Apa da Guma na jihar, tsakanin ranekun Laraba zuwa Lahadi, inda ’yan bindigar suka kone gidaje da sauran kadorori.

A nasa bangare, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bukaci a yi dukkan kokari wajen kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar. Ya kuma umarci jami’an tsaro da su inganta sa ido ta kowanne bangare da kuma gaggauta sake nazarin dabarun tsaro a yankunan da matsalar ta shafa.

©(Fa’iza Mustapha)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Hare-haren ’yan bindiga ya yi sanadin mutuwar mutane 134 a Nijeriya”