June 3, 2024

Hare-haren da Isra’ila ta kai kan Aleppo na kasar Siriya ya janyo hasarar rayuka da dukiya

 Litinin, 03 Yuni 2024 12:34 AM

Jaridar ahlulbaiti ta ruwaito Kamfanin dillancin labarai na sana Dake kasar siriya cewar,

Gwamnatin kasar Isra’ila ta kaddamar da wani sabon harin wuce gona da iri kan birnin Aleppo da ke arewa maso yammacin kasar Syria, wanda ya haddasa hasarar rayuka da kuma asarar dukiya.

Kamfanin dillancin labaran SANA na kasar Siriya ya nakalto majiyar sojan da ba a bayyana sunanta ba, ta ce sabon harin ta sama ya fito ne daga kudu maso gabashin Aleppo jim kadan da tsakar daren  Litinin.

Rahoton ya kara da cewa harin na Isra’ila ya kai wasu wurare a kusa da birnin Aleppo, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da yin barna.

Sanarwar da majiyar sojin Syria ta fitar ba ta fayyace adadin wadanda suka mutu a harin ba da kuma jami’an soji ne ko kuma fararen hula.

Wannan sabon harin na Isra’ila ya zo ne bayan hare-haren da Isra’ila ta kai a ranar Larabar da ta gabata ta kai hari a wasu wurare daban-daban a fadin kasar ta Siriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane hudu ciki har da wani yaro.

 

Mai fassara Hadiza Mohammed.

 

 

SHARE:
Tarbiyyan Yara 0 Replies to “Hare-haren da Isra’ila ta kai kan Aleppo na kasar Siriya ya janyo hasarar rayuka da dukiya”