May 19, 2023

Har yanzu ana gwabza fada tsakanin dakarun janar-janar dake rikici a kasar.

Rahotanni daga Sudan na cewa har yanzu ana gwabza fada tsakanin dakarun janar-janar dake rikici a kasar.

Bayanai sun ce ana ci gaba da luguden wuta a wasu yankuna na birnin Khartoum, yayinda fada ya sake barkewa a kusa da sansani sojoji da ke kudancin birnin kasar.

Sojoji na amfani da manyan makamai musamman atilary wajen fatatakar dakarun RSF daga inda suke zama a yankunan birnin Khartoum, da kuma wasu birane irinsu Bahri da Omdurman.

Rikicin Sudan wanda ya barke a ranar 15 ga watan Afrilu da ya gabata ya lakume rayuka fiye da 800, a cewar bayanai.

Hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta ce, tana bukatar akalla dala biliyan uku domin gudanar da ayyukan agaji ga miliyoyin mutane da rikicin Sudan ya shafa

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Har yanzu ana gwabza fada tsakanin dakarun janar-janar dake rikici a kasar.”