March 16, 2023

Hannayen Jari A Kasuwannin Turai Sun Fadi, Sakamakon Durkushewar Bankuna A Amurka

Kasuwar hada- hadar kudi ta Dow Jones a Amurka ta fuskanci koma baya a cinikinta na ranar Laraba.

Hannun jarin bankin Swiz ya fadi warwas bayan wanda ya fi zuba jari a cikin bankin ya ce ba zai sake ba shi tallafi ba.

Wannan na zuwa ne bayan durkushewar bankin Silicon valley na Amurka a kwanakin baya.

An rufe bankin Silicon Valley Bank (SVB) a ranar 10 ga watan Maris, wanda ya zama banki mafi girma da aka rufe a Amurka, tun bayan barkewar rikicin hada-hadar kudi a shekara ta 2008.

Daga bisani kuma a ranar 12 ga wata, an rufe wani bankin kasar na daban da ake kira Signature Bank, sakamakon “hadarin dake tattare da tsarinsa”.

Sakamakon haka, darajar takardun hannayen jarin bankuna ta fadi warwas.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Hannayen Jari A Kasuwannin Turai Sun Fadi, Sakamakon Durkushewar Bankuna A Amurka”