January 30, 2024

Hamas : Sai An Tsagaita Wuta, Zamu Fara Shawarwarin Sakin Wadanda Ake Garkuwa Dasu

Kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa tana da niyyar yin shawarwari, amma sai an tsagaita wuta za’a fara batun sakin wadanda ake garkuwa dasu.

Taher al-Nounou, wani babban jami’in Hamas, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa hakan bayan ganawa da jami’an Amurka da Isra’ila da na Qatar da kuma Masar.

Da zarar an daina fada, “za a iya tattauna sauran bayanai”, ciki har da sakin ‘yan Isra’ila dari da har yanzu suke hannunsu a Gaza, inji jami’in na Hamas.

A wani labarin kuma, bisa sabon rahoton da ma’aikatar lafiya ta Hamas ta fitar, jiya Litinin, ta ce, an kashe falasdinawa 26,637 a Gaza tun farkon yakin a ranar 7 ga watan Oktoba.

Isra’ila dai na ci gaba da kai hare-harenta a zirin Gaza, kuma har yanzu ana zaman dar-dar a yankin yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye da kuma kan iyakar Lebanon.

 

©VOH

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Hamas : Sai An Tsagaita Wuta, Zamu Fara Shawarwarin Sakin Wadanda Ake Garkuwa Dasu”