January 25, 2024

Haifaffen Ka’aba A Watan Rajab!

 

Haifaffen Ka’aba shine Imam Ali (AS), masadir dayawa na shi’a da sunni sun ruwaito wannan hadisa da ta faru na haihuwan Imam Ali (AS) a cikin ɗakin Allah, a ranar 13 ga watan Rajab.

Allama Majilisi ya naƙalto masadar 16 na sunni da suka hakaito wannan hadisa, haka nan ya naƙalto masadir 50 na shi’a da suka kawo hadisar, shi yasa hadisan haihuwar Imam Ali (AS) a cikin Ka’aba sun kai haddin tawatir.

Sadouq ya ruwaito a littafin sa الأمالي والمعاني الأخبار daga Zaidu bin Ƙa’anab yace: “Na kasance zaune tare da Abbas bin Abdulmutallib a jikin ɗakin Ka’aba sai muka ga Faɗimatu bintu Asad ta tunkaro tana ɗauke da juna, tana cewa : Ya Allah hakika ni mai imani ce da kai, da abinda ƴan aiken ka suka zo da shi na daga litattafai, kuma ni mai gaskata maganganun kakana Ibrahim khalil ce, don wanda ya gina wannan ɗaki, don wannan abin haihuwa da ke cikina ka sauƙaƙa min haihuwa ta, Yazid yace: Nan take muka ga ginin ɗakin Ka’aba yana tsagewa, sai Faɗimatu bintu Asad ta shiga ciki, sai ginin ɗakin ya haɗe” Munyi ƙoƙarin buɗe kwaɗon da ke kofar ɗakin amma yaƙi buɗuwa, tsawon kwanaki huɗu Faɗimatu bintu Asad tana ciki sannan ta fito tare da ɗanta”

Abune sananne ɗakin Ka’aba yana da ƙofa da ake iya shiga ko fita daga cikinsa, amma a lokacin da ta yi addu’ar ba ƙofar ne ya buɗu ba, ginin ne ya tsage, a nan Allah na so ne ya nuna maka saɓanin al’ada Mu’ujiza, saboda kada wata rana a samu wani da zaice ai iska ne ya tura kofar shi yasa ta buɗe.

Babban Abin Mamakin Shine: Har zuwa yau alamun tsagewan yana jikin ɗakin ka’aban, duk da sake ginin da aka sha yi tsawon ƙarnoni da duka gabata, kuma kafinsa da bayansa ba’a samu wani da aka haifa a cikin Ka’aba ba.

Tsawon kwanakin da ta yi a cikin ɗakin Imam Ali (AS) bai kama nono ba, baici komai ba kuma idanu a rufe, sai ranar da ta fito Annabi Muhammad (S) ya zo ya karɓe shi sannan ya buɗe idanu, farkon wanda Imam Ali (AS) ya yi tozali da shi shine Annabi Muhammad (S), sannan Annabi ya sanya harshensa a cikin bakin Imam Ali (AS), Imami ya rinƙa tsotsa, Allah kaɗai ya san sirrukan da ya tsotsa.

Ina taya ɗaukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwansa Haifaffen Ka’aba Imam Ali (AS), wanda ya faru a 13 ga watan rajab.

© Sheikh Emran Darussalam

SHARE:
Makala 0 Replies to “Haifaffen Ka’aba A Watan Rajab!”