Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

August 14, 2021

Habib Bin Mazahir

Muhammad Auwal Bauchi

 

Habib bn Mazahir al-Asadi ya kasance daga cikin kabilar Banu Asad, duk da cewa ba a yi bayanin cikakken lokacin da aka haife shi ba, to  amma dai abin da aka tabbatar  shi ne cewa  a lokacin da yayi shahada a Karbala ya kasance yana da shekaru 75 a duniya. Ya kasance daga cikin sahabban Ma’aiki (s.a.w.a) kana kuma daga cikin zababbun shahabban Imam Amirul Muminin Ali (a.s) ya kasance cikin dukkanin yakukuwan da Imam Ali (a.s) ya yi, kamar yadda kuma ya kasance daga cikin sahabbai kana masoya Imam Husain (a.s) wadanda suka ba da jininsu don kare shi da kuma kare yunkurinsa na Karbala.

Tun yana karami, Allah Ya sanya wa Habib tsananin kaunar Imam Husain (a.s) wanda ya kasance kusan tsararsa a bangaren shekaru a wancan lokacin. Irin wannan kaunar da yake nuna wa Imam Husain (a.s) ne ma ya sanya Manzo (s.a.w.a) yake tsananin kaunarsa. An ruwaito cewa wata rana Manzon Allah (s.a.w.a) yana tafiya tare da daya daga cikin sahabbansa mai suna Mazahir (wato baban Habib). Da suka zo wani waje sai Manzo ya zauna a kasa. Sai ya kira dan Mazahir din wato Habib, ko da yaron ya zo sai Manzo (s.a.w.a) ya rungume shi yana sumbantarsa. Wannan yanayi dai ya ba wa Mazahir mamaki, don haka sai ya tambayi Annabi (s.a.w.a) me dan nasa yayi da ya cancanci irin wannan nuna kaunar daga wajensa. Nan take idanuwan Ma’aiki (s.a.w.a) suka ciko da kwalla yana fadin cewa: Ya Mazahir! Lokacin da muke tafiya na lura Habib, yana tafiya a bayan Husain, duk inda ina Husain ya taka shi ma ya kan bi wajen don nuna girmamawa ga Husain. Ya Mazahir, wannan Habib din wata rana zai taimaka wa dana Husain.

Wannan yana nuni da irin matsayin da Habib yake da shi ta yadda har an sanar da Ma’aiki irin rawar da zai taka wajen kare Musulunci a nan gaba.

Habib ya tashi ne a gidan da ya gaji jaruntaka da karimci da cika alkawari da dai sauran siffofi masu kyau kuma na kamala, wanda irin wadannan siffofi su ne suka sanya ya zama abin yarda a wajen Imam Husain (a.s) kafin haka kuma a wajen mahaifinsa Imam Amirul Muminin (a.s).

A hakikanin gaskiya kaunar Ahlulbaiti da kuma sadaukarwa saboda su ba wani bakon abu ba ne a wajen Habib da kuma zuriyarsa don kuwa ‘yan’uwansa biyu wato Yazid da Ali su ma sun kasance daga cikin wadanda suka yi shahada tare da Imam Husain (a.s) a Karbala. Wasu riwayoyin sun bayyana cewar: Lokacin da abubuwa suka fara yin tsanani a Karbala, Imam Husain (a.s) ya gaya wa sahabbansa cewa: “A cikinku duk wanda yake tare da mace, to ya koma da ita wajen iyayenta”. Sai Ali bn Mazahir (dan’uwan Habib) ya mike ya ce: Ko me ya sa haka, Ya Shugabana! Sai Imam Husain (a.s) ya ce masa: Saboda bayan an kashe ni za a kama matayena a matsayin fursunonin yaki. Ina tsoron kar a kama muku matayenku a matsayin fursunonin yaki. Don haka sai Ali ya tashi ya tafi haimarsa ya gaya wa matarsa abin da Imam Husain (a.s) ya ce, sai ta tambaye shi cewa to  yanzu me kake son yi, sai ya ce mata: Ki tashi in mai da ke wajen iyayenki. Sai ta ce masa: A’a wallahi, mu zauna, ku kuna tausayawa (kuna ba da kariya ga) maza (na daga zuriyar Annabi) mu kuma muna tausayawa wa mata. Don haka sai ya koma wajen Imam Husain (a.s) ya gaya masa cewa: Ba’asadiyya ta ki yarda, face ta ci gaba da zama da ku. Don haka sai Imam Husain (a.s) ya gode musu da musu fatan alheri.

Don haka kaunar Imam Husain (a.s) wani lamari ne da ya sami gindin zama cikin zukatan iyalan Habib musamman ma shi Habib din wanda irin wadannan siffofi da yake da su ne ya sanya ya zamanto abin kauna da kuma yardar Imam Amirul Muminin (a.s), wanda hakan ya sanya ya kan sanar da shi wasu ilmummuka wadanda bai sanar da sauran sahabbansa ba.

Habib bn Mazahir ya kasance abokin Imam Husain (a.s) na kurkusa tun suna kanana. A lokacin da Imam Ali (a.s) ya mayar da helkwatar halifancinsa daga Madina zuwa Kufa, shi ma Habib ya koma garin na Kufa, inda ya zauna a can kuma ya zamanto daga cikin manyan garin. Irin wannan kusaci da yake da shi da Imam Husain (a.s) da kuma kaunar da yake masa ne ma ya sanya shi ne mutumin farko, daga cikin mutanen Kufa, da ya fara rubutawa Imam Husain (a.s) wasika da kiransa da ya zo garin Kufan don jagorantar  al’umma.

Duk da cewa Habib ya taka gagarumar rawa a lokacin halifancin Imam Amirul Muminin (a.s) musamman cikin yakukuwan da yayi, to sai dai suna da kuma tauraruwarsa ta  fi  fitowa fili ne yayin yunkurin Ashura na Imam Husain (a.s).

Don haka bari mu dan yi dubi ko da a  takaice ne dangane da irin rawar da ya taka a wannan fage da kuma irin yadda ya kasance mai cika alkawari da kara tabbatar da wilayarsa ga Ahlulbati (a.s)  duk kuwa da irin tsananin da ake ciki.

Bayan da Imam Husain (a.s) ya kaddamar da yunkurinsa na tsarkake Musulunci daga dauda da kazantar da Umayyawa suka shafa masa daga garin Makka, da kuma wasikun da ya dinga samu daga wajen mutanen Kufa kan ya zo don ya jagorance su. Imam Husain ya aika da dan baffansa Muslim bn Akil zuwa Kufan don gane masa yanayin da ake ciki.

Bayan isar Muslim da kuma irin yadda lamurra suka sauya bayan isar Ubaidullah bn Ziyad garin da nufin murkushe wannan yunkuri na mutanen Kufa, lamarin da ya sanya mutanen Kufan juyawa da baya. Daga karshe dai Ubaidullah ya ba  da umurnin rufe garin ta yadda babu wani da zai shiga ko fita ba tare da sani da kuma izininsa ba.

Wannan yanayi ya sanya Habib bn Mazahir cikin tsananin kumci da damuwa don kuwa a loakcin bai ma san halin da Imam Husain (a.s) din yake ciki don kuwa Ibn Ziyad ya sanya ‘yan leken asirinsa suna ta  yada jita-jita da kararraki don dai a razana mutane da kuma kashe musu gwiwan tunanin taimakon Imam Husain (a.s).

Zamu ci gaba…

SHARE:
Raruwar Magabata One Reply to “Habib Bin Mazahir”
Ahlul Baiti
Ahlul Baiti

COMMENTS

One comment on “Habib Bin Mazahir

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *