August 15, 2021

Habib Bin Mazahir

Ci gaba daga rubutun da ya gabata…

A cikin irin wannan yanayin ne sai ga wasikar Imam Husain (a.s) zuwa gare shi (Habib) yana kiransa da ya zo ya same shi. A cikin wasikar dai Imam Husain (a.s) ya rubuta masa cewa:

“Daga wajen Husain bn Ali zuwa ga masani Habib bn Mazahir. Bayan haka, Ya Habib, ka san irin kusancinmu da Manzon Allah (s.a.w.a), kai din nan ka fi waninka saninmu. Kai din nan ma’abocin dabi’u da kishi ne, don haka kada ka yi mana rowar kanka. Sakayyarka na wajen Kakanmu, Manzon Allah”.

Lokacin da Habib bn Mazahir ya samu wannan wasika ta Imam Husain (a.s) ya sanar da matarsa abin da ta kumsa. Na take cikin kauna ta bukace shi da ya gaggauta tafiya don taimakon Imam Husain (a.s).

Daga nan sai Habib ya fara shirin tafiya wajen Imam Husain (a.s), to sai dai kuma cikin sirri ba tare da an sani ba don kada labari ya  yadu Ibn Ziyad ya cutar da shi. To sai dai duk da hakan labarin ya dan fara fita inda kabila da danginsa suka nufo wajensa don neman jin gaskiya labarin. Habib dai ya musanta musu wannan labarin inda ya ce babu gaskiya cikin hakan. Bayan tafiyarsu dai matarsa wacce ta ji yadda tattaunarwar ta su ta kasance ta zo wajensa inda ta tambaye shi wai shin da gaske ne ba zai tafi din ba. To don ya jarraba ta sai ya ce mata lalle ba zai tafi ba. Nan take ta fashe da kuka tana ce masa: Ashe ka mance da maganar kakansu Annabi (s.a.w.a) a kansa ne da dan’uwansa Hasan inda ya ke cewa: Wadannan ‘ya’ya nawa su biyu, su ne shugabannin matasan Aljanna, sannan kuma su imamai ne, sun mike ko kuma ba su mike ba. A halin yanzu ga manzon Husain ya zo maka da wasikar neman taimakonka, amma ka ki ka amsa masa?. Sai Habin ya ce mata: Ina tsoron abin da zai sami ‘ya’yana na zama marayu, sannan ke kuma ki zama bazawara a bayana. Sai ta  ce masa: Allah Madaukakin Sarki Shi zai kula da mu kuma Ya isar mana, kuma madalla da kasantuwarsa mai kula da mu. Lokacin da Habib ya fahimci irin wannan imani nata da kuma dagewa kan cika alkawari ga iyalan gidan Annabi, don haka sai ya gobe mata da kuma sanar da ita hakikanin abin da ke cikin zuciyarsa na tafiya wajen taimakon Imam Husain (a.s). Sai matar ta ce masa to ina da wata bukata a wajenka. Ya ce mata mece ce bukatar ta ki. Sai ta ce: Ya Habib, don Allah, idan har ka gana da Husain, ka sumbanta min hannunsa a madadina, sannan ka isar min da gaisuwa  ta  zuwa gare shi.

Daga nan sai Habib ya umurci wani bawansa amini da ya kama dokinsa ya tafi da shi can wajen gari ya jira shi a can, idan har an tambaye shi ya ce zai kai shi kiwo ne. Lokacin da yamma ta yi sai Habib ya sulale ya nufin inda dokin nasa yake. Lokacin da ya isa can, ya hau dokin, sai yayi bankwana da bawan nasa ya ce masa: Tafi abinka, na ‘yantar da kai. Nan take bawan ya sa kuka yana cewa: Ya kai shugabana ba ka kyauta min ba. Na kasance mai maka hidima shekaru aru-aru. A halin yanzu na sami damar yin hidima wa dan Fatima al-Zahra (a.s), amma kana ce min in tafi. Me ya sa kake hana ni waje a cikin Aljanna? Wadannan kalmomi sun sosa ran Habib, don haka sai ya bukace shi da ya hau bayan doki su tafi tare inda suka isa Karbala tare.

A daidai wannan lokacin da Habib yake ta shirin zuwa Karbala, shi kuma Imam (a.s) yana ta shirin raba tutoci guda goma sha biyu da ya tsara su, sai aka ga ya ajiye guda daya ko da aka tambaye shi ta waye sai ya ce mai ita yana nan tafe.

Ana cikin hakan ne sai aka ga kura tana tasowa daga bangaren garin Kufa, wato Habib da bawansa ne suka doso Karbala. Don haka sai Husain da sahabbansa suka nufi inda suke don yi musu maraba. Lokacin da Habib ya iso ya sauka a kan dokinsa ya nufo inda Imam Husain (a.s) yake yana kuka yayi masa sallama, Imam da sahabbansa suka amsa masa. Lokacin da Zainab (a.s) ta ji zuwan Habib din sai ta tambaya wane ne wannan mutumin da ya zo din? Sai aka ce mata: Habib bn Mazahir ne. Sai ta ce: Ku isar masa da sallamata. Lokacin da aka gaya masa nan take Habib ya fashe da kuka yana fadin cewa: Ni ne wa da har ‘yar Amirul Muminin Ali za ta gaishe ni.

Riwayoyi sun bayyana cewar Habib ya iso sansanin Imam Husain (a.s) ne ranar shida ga watan Muharram, don haka bayan isowarsa yayi iyakacin kokarinsa wajen janyo wasu mutane daga cikin ‘yan kabilarsa na Banu Asad da suke cikin rundunar Ibn Ziyad inda ya sami nasarar mai do da wasu daga cikinsu zuwa sansanin Imam Husain (a.s) bayan da ya kiraye su zuwa ga taimakon dan ‘yar Ma’aiki (s.a.w.a) har zuwa ranar Ashura, ranar  karshe ta Imam Husain (a.s) da mabiyansa.

A wannan rana sahabban Imam Husain (a.s) daya bayan daya suna tafiya filin daga don yakar makiya bayan yaki na wani lokaci, daya bayan daya sunata yin shahada.

Ganin haka sai Habib bn Mazahir ya taho wajen Imam Husain (a.s) ya ce masa: Ya Shugabana! Ka ba ni izinin fita filin daga. Ka bari in sadaukar da raina saboda Musulunci.

Imam Husain (a.s) ya ce masa: Ya Habib, Ya tsohon abokina, ka zauna tare da ni, don kuwa kana kwantar min da rai.

Habib dai ya ci gaba da matsawa. Daga karshe dai Imam Husain (a.s) ya ba shi izinin fita. An ce Imam Husain (a.s) shi ya rike masa dokinsa ya  hau, inda ya shiga fagen daga ya ta bugun makiya da kashe su har lokacin da suka yi masa taron dangi, suka cimmasa ya fadi a kasa.

Ganin haka Imam Husain (a.s) ya ruga da gudu ya tafi wajensa. Koda Habib ya ga Imam Husain sai ya ce masa: Ya dan Manzon Allah, ka gafarta min saboda gazawar da na yi wajen sadaukarwa sama da wannan ran da nake da shi saboda kai da kuma Musulunci”. Imam Husain (a.s) ya dauki Habib ya rungume shi yana kuka. Da haka ne dai Habib yayi shahada a kafadar Imam Husain (a.s).

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Habib Bin Mazahir”