October 5, 2021

Gwamnoni 8 Na Yankin Tafkin Chadi Sun Gana A Kasar kamaru

Babangida Babagana


Gwamnoni 8 na yankin tafkin Chadi sun yi zama garin Yaunde, babban birnin Kamaru a jiya Litinin don tattaunawa kan matsalolin tsaro dake addabar yankin.

Zaman tattaunawar ya shamu shirin kungiyoyi da suka hada da kungiyar hadin kai ta Afirka, majalisar dinkin duniya da ma sauran su. Kana kuma gwamnatin Kamaru ta dau nauyin gudanarwa tare da hadin gwiwa da kungiyar gwamnonin yankin na tafkin Chadi.

Shida daga cikin gwamnonin wadanda suka hada da gwamna Babagana Umara Zulum na jahar Borno daga Nijeriya, Issa Lamine na Diffa daga Nijar, Midjiyawa Bakari daga Kamaru, Abate Edii Jean shima daga Kamaru, Mahamat Fadoul Mackaye daga Chadi, da kuma Amina Kodjyana daga Chadi, a bangare guda kuwa gwamnonin Yobe da Adamawa sun aika da wakilai.

A wani bayani na mai bada shawara na musamman ga Gwamna Zulum, Malam Isa Gusau ya bayyana cewa fitayi ministan Kamaru Joseph Dion Ngute ne ya bude taron sannan bayani daga bakin Mayor na Yawunde inda suka tattauna kan lamarin tsaro da kuma mayar da hankali kan agajin jin ‘kai a yankin na tafkin Chadi.

Gwamna Zulum a gudunmawar da ya bayar yayin taron yayi kira da babban murya kan kara karfafa tsaro a iyakokin kasashen.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Gwamnoni 8 Na Yankin Tafkin Chadi Sun Gana A Kasar kamaru”