May 11, 2023

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za a fara daukar bayanan dukkan masu hakar ma’adanai da sauran masu sana’o’in hannu

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za a fara daukar bayanan dukkan masu hakar ma’adanai da sauran masu sana’o’in hannu da suke da rijista a fadin kasar a kokarin tabbatar da ganin an dakile ayyukan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
Ministan bunkasa harkokin ma’adanai da karafa Architect Olamilekan Adegbite ne ya tabbatar da hakan jiya Laraba 10 ga wata lokacin bikin kaddamar da kamfanin sarrafa kwal a garin Mopa dake jihar Kogi a arewa ta tsakiyar Najeriya.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ministan ya ce yanzu haka gwamanti ta bullo da wani tsari da zai taimaka wajen rage ayyukan hakar ma’adanai da yin safarar su ta haramtacciyar hanya.
Wannan mataki dai kamar yadda ministan ya fada zai kara budawa gwamnati kafofin samun kudin shiga da samar da ayyukan yi da inganta muhalli kana da kyautata zamantakewar al’ummmomi.
Ministan bunkasa harkokin ma’adinai na tarayyar Najeriya ya ce ma’aikatarsa tana bayar da kulawa sosai ga masu hakar ma’adinai da suke da rijista, saboda hadin kansu ne gwamnati za ta samu cimma burinta wajen bullo da dabaru da za su kawo karshen ayyukan ta’addanci da suka addabi wasu sassan kasar wadanda suke da nasaba da matsalolin rashin aikin yi.
Ya ce daukar bayanan masu hakar ma’adinai babbar hanya ce da za ta iya kawar da bara-gurbi daga cikin masu sana’ar.
A kan kamfanin sarrafa kwal din kuwa Mr Olamilekan Adegbite ya ce makasudin zabar yankin na Mopa a matsayin wurin kaddamar da wannan masana’anta shi ne sabo da yanki yana daga cikin yankunan da suke da arzikin kwal a shiyyar arewa maso yamma zuwa kuma yammacin jihar Kogi .
Ministan ya ce yankin na Mopa yana da daruruwan kananan masu sarrafa kwal, wanda samar da kamfanin kuma zai ba su damar shiga masana’antar don sarrafa kwal da tacewa cikin sauki.
Shi dai wannan tsarin daukar bayanai ya kunshi daukar hotuna na ’yan yatsu baya ga bayanai a kan asali.
Auwal Bala Durumin Iya kwararre wajen ilimin binciken laifuka kuma malami a jami’ar fasaha dake Wudil a jihar Kano ya shaidawa CRI cewa zai yi wahala a samu nasarar da ake nema dari bisa dari duk kuwa da cewa mataki ne mai kyau.
“Wannan hanyar ba za ta tabbatar ta rage satar kayayyakin albarkatun kasa a Najeriya ba, dalili kuwa shi ne ko da kasar Saudiya da suke da na’urori manya masu inganci da kwararru wajen bibiyar bayanan sirrin mutum, amma hanyar tana ba su wahala sosai, saboda yanzu akwai likitocin da suke fyede fatar dan yatsar mutum yadda koda ya dangwala hannun sa ba za a ga bayanansa ba, kamar misalin irin mutanen da aka dawo da su Najeriya daga Saudiya suna komawa bayan an yi masu tiyatar fatar ’yan yatsu ba tare da an gano su ba”.

©cri (Garba Abdullahi Bagwai)

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za a fara daukar bayanan dukkan masu hakar ma’adanai da sauran masu sana’o’in hannu”