August 9, 2021

GWAMNATIN TARAYYA TA TSAYAR DA RANAR YIN RIGAKAFIN KORONA A KARO NA BIYU

Daga Musa Geidam

Hukuma ta musamman kan yaki da annobar korona a Najeriya ta aiyana ranar 16 ga wata Agusta matsayin ranar da za’a fara allurar rigakafin korona a karo na biyu.

Tun a karon farko dai, ranar Talata, 10 ga watan Agusta ne ranar da aka aiyana don fara rigakafin amma daga bisani sai aka dage a daren lahadi, inda aka mayar da ranar 16 ta kasance ranar da za’a fara rigakafin a maimakon ranar 10 kamar yadda aka tsayar da farko.

Hukumar dai ta bayyana cewa ta canza ranar fara rigakafin ne saboda bama hukumar NAFDAC ta gama shirye-shiryenta a tsanake.

Za’ayi amfani da allurar “Moderna vaccine” ne wurin yin rigakafin wanda aka shigo da ita daga kasar Amurka a ranar 2 ga watan Agusta.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “GWAMNATIN TARAYYA TA TSAYAR DA RANAR YIN RIGAKAFIN KORONA A KARO NA BIYU”