September 8, 2021

Gwamnatin Tarayya Ta Karo Alluran Rigakafin Korona 1,123,200

Daga Balarabe Idriss


Gwamnatin tarayya ta karo allaurar rigakafin korona na “Johnson & Johnson” wanda adadin su yakai kimanin 1,123,200 don yi ma yan kasar.

Daraktan kiwon lafiya na “Primary Health Care Development Ageny” Faisal Shuaib ya sanar da manema labarai cawa an karbi sabon samfurin alluran rigakafin ya iso ne ranar lahadi da dare.

Inda ya bayanna cewa hukumar NAFDAC tuni ta dauki samfurin kuma yanzu haka tana kan gudanar da bincike akansa saboda tabbatar da ingantaccen rigakafi ga al’ummar Najeriya.

Ya kuma kara da cewa zuwa yanxu mutane kimanin 3,600,858 ne akayi musu rigakafin na Korona.
Kana kuma yayi karin bayani cewa daga cikin adadin da ya ambata, mutane 2,551,738 ne akayi musu rigakafin da samfurin AstraZenece a yayin da mutane 1,049,120 kuma aka yi musu da samfurin Moderna.

Ya kuma ce sun karbi sakonnin mutane da dama kan yiwuwar kamuwa da cutar bayan an riga anyima mutum rigakafinta, amma sai dai ya bayyana cewa cutar hatsarinta yafi yawa ga mutumin da ba’a yimasa rigakafin ba.

Ya nuna cewa rigakafin na hana tsanantar cutar ko da kuwa ta kama mutum da kuma karanta hatsarin mutuwa.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Gwamnatin Tarayya Ta Karo Alluran Rigakafin Korona 1,123,200”