March 30, 2023

Gwamnatin Rasha Ta Fara Jarraba Makaman Linzaminta Samfurin Yars Mai Keta Nahiyoyi

 

Gwamnatin kasar Rasha ta bata sanarwan cewa ta fara jarraba makamanta masu linzami kuma wadanda suke keta nahiyoyi bayan da ta fice da yarjeniyar takaita makaman nukliya da kasar Amurka.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan tsaron kasar Rasha yana fadar haka a shafin telegram na ma’aikatar tsaron kasar ya kuma kara da cewa an fara gwajin makaman masu linzami samfurin Yars ne tare da sojojin 3000 da kuma kayakin aiki kimani 300.

Labarin ya kara da cewa kasar Rasha tana son nuna wa duniya irin karfin makaman masu linzami kuma mafi keta nahiyoyin da take da su. Bayan ficewa daga yarjeniyar takaita makamai nukliyar da Amurka.

Makamai masu linzami samfurin Yars dai ko kuma ICBM yana iya keta nahiyoyi har na tsawon kilomiya 11,000, banda haka yana iaya daukar wasu kananan makamai masu linzami akalla 3 a lokaco guda ko kuma 6 a lokaci guda. Zuwa wasu wuraren,

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Gwamnatin Rasha Ta Fara Jarraba Makaman Linzaminta Samfurin Yars Mai Keta Nahiyoyi”