April 9, 2023

Gwamnatin Nijar Ta Zaftare Kudin Aikin Hajjin Bana

 

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ta sanar da rage kudin aikin hajjin bana daga kudin sefa Miliyan 3,603,840 zuwa 3,258,733 kwatankwacin ragin sefa 345,105, kamar yadda ma’aikatar kasuwanci ta kasar ta sanar.

Babu dai wani karin bayyani akan dalilin samun wannan ragin da aka samu, amma a cen baya an sha sukar farashin aikin hajjin na bana da cewa ya yi matukar tsada idan aka kwatanta da na sauren kasashen yankin.

Farashin da gwamnatin kasar ta sanar da farko ya karu da sefa dubu 400 idan aka kwatanta shi da ba bara.

A bara dai an fuskanci jinkiri wajen jigilar mahajatta a Nijar, yayin da wasu 134 basu ma samu tafiyar zuwa Saudiyya ba saboda matsalolin da aka samu.

A bana dai Saudiyya ta ware wa Nijar kujera 15,891 kusan linkin adadin na bara.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Gwamnatin Nijar Ta Zaftare Kudin Aikin Hajjin Bana”