July 19, 2023

​Gwamnatin Najeriya Tana Tunanin Kara Albashin Ma’aikata Har Zuwa Naira Dubu 200

 

Gwamnatin tarayyar Najeriya zata kara albashin har zuwa naira dubu 200 a matsayin mafi karancin albashi. Jaridar Leadership ta Najeriya ta bayyana cewa an tattauna wannan batun a taron majalisar tattalin arziki ta kasa kuma har an kafa kwamiti don duba yiyuwan kara albashi ga ma’aikata har zuwa wannan adadin idan shugaban kasa ya amince da hakan.

Kafin haka dai shugaban Tinubu ya bayyana cewa babu laifi a kara yawan albashin ma’aikata amma bai bayyana zuwa wani adadi ne zai kai ba.

Karan farashin makama shi, da faduwar darajar Naira da wasu al-amura da dama sun kara matsalolin tattalin arzikin da mutanen kasar suke fama da su, wanda ya sa dole ne gwamnati ta kara albashin ma’aikata.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Gwamnatin Najeriya Tana Tunanin Kara Albashin Ma’aikata Har Zuwa Naira Dubu 200”