December 23, 2023

Gwamnatin Najeriya ta kammala aikin gyaran matatar man dake Fatakwal

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, an kammala manyan ayyukan gyaran injunan dake kamfanin mai na Fatakwal, daya daga cikin tsoffin matatun tace man fetur a kasar.

Karamin ministan albarkatun man fetur na kasar Heineken Lokpobiri ne, ya shaidawa manema labarai hakan a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers mai arzikin man fetur. Yana mai cewa, wuta ya fara fita a matatar da ke da karfin tace ganga dubu 210 na danyen mai a kowace rana

Matatar mai ta Fatakwal, mai dauke da sassan tace mai guda biyu, an rufe ta ne a watan Maris din shekarar 2019, yayin kashi na farko na ayyukan gyaran matatar, a wani bangare na kudirin gwamnati na farfado da sabunta muhimman ababen more rayuwa. Ana sa ran aikin gyare-gyaren, zai bunkasa aikin tace mai a cikin gida da kuma rage dogaron da kasar ke yi kan man da ake shigowa da shi daga kasashen waje.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Gwamnatin Najeriya ta kammala aikin gyaran matatar man dake Fatakwal”