April 26, 2023

Gwamnatin Najeriya Ta Fara Kwasar Yan Kasarta Daga Sudan

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto hukumar “Yan Najeriya a kasashen waje” ko NiDCOM tana fadar haka a shafinta na twitter, ta kuma nuna hotunan motocin da aka kawo don kwasar yan Najeriya, wadanda galibinsu daliban jami’o’ii ne, da kuma wasu hotunan suna nuna rijistan yan Nigeria a ofoshin jakadancin Najeriya dake Karthum babban birnin kasar.

Labarin ya kara da cewa bayan kwasarsu zuwa wani wuri a kan iyakar kasar Sudan da Masar ne, za’a kwasosu da jiragen sama zuwa gida Najeriya.

Kimani mako guda kenan da barkewar yaki a kasar Sudan tsakanin bangarorin sojojin kasar, kuma kokarin tsagaita budewa juna wuta har sau uku sun kasa tsaida yakin ya zuwa yanzu mutane kimani 500 suka rasa rayukansu a yayinsa wasu 4,100 suka ji rauni.

Amma Volker Perthes jakadan MDD a Sudan ya fadawa Kwamitim tsaro na majalisar a jiya Talata kan cewa babu wata alama ta sasantawa tsakanin bangarorin biyu masu yaki.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Gwamnatin Najeriya Ta Fara Kwasar Yan Kasarta Daga Sudan”