August 30, 2021

Gwamnatin Kano ta Ƙarawa daliban jihar Hutun Mako Guda

Daga Baba Abdulƙadir
Ma’aikatar llimi ta jihar kano ta daga ranar komawa makaranta a dukkanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu zuwa sati mai zuwa.
Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Malam Sunusi Sa’id Kiru yace, an kara mako daya na komawa makaranta dan nufin dai daita tsarin ranakun kalandar a sakamakon rushewar da yayi, duba da Annobar Korona a jihar,
Jami’in hulda da jama’a, na ma’aikatar Ilimin ta jihar kano Malam Aliyu Yusuf shi ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yau litinin.
Kazalika ya ce, baya da haka dukkanin daliban makarantun kwana zasu koma ranar 5 ga wata zuwa 12 ga watan Satumba 2021, sannan kuma ranar 6 ga wata masu zuwa jeka ka dawo  za su koma zuwa 13 ga wata” a cewar sanarwar.
“Kwamishinan ya bayyana jindadinsa tare da fatan iyaye za su bada hadin kai da kuma kulawa da ‘ya’yan nasu na dan wani lokaci”, a cewar ma’aikatar Ilimin.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Gwamnatin Kano ta Ƙarawa daliban jihar Hutun Mako Guda”