Gwamnatin Jumhuriyar Niger Ta Musanta Korar Jakadan Najeriya Daga Kasar

Gwamnatin Jumhuriyar Niger ta musanta cewa ta kori jakadan kasar Nigeriya daga kasar kamar yadda wata majiyar ma’aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana a jiya jumma.
Jaridar Daily Trust ta Nigeriya ta bayyana cewa akwai rashin fahintar yadda al-amura suke tafiya a jumhuriyar Niger dangane da korar jakadun wasu kasashen daga kasar.
Kafin haka dai ma’aikatar harkokin wajen kasar a jiya Jumma’a ta bada sanarwan cewa ta bawa jakadun kasashen Naijeriya da kuma na wasu kasashen yamma sa’oii 48 su fice daga kasar.
Amma wata majiyar gwamnatin sijojin kasar a yau asabar ta bada sanarwna cewa bata kori jakadan Najeriya daga kasar ba, kuma ta kara da cewa jakadan kasar Faransa ne ta kora saboda yak i amsa gayyatar ma’aikatar harkokin wajen kasar na tattaunawa da shi a kan wasu al-amura.
Labarin ya kara da cewa jakadun kasashen Faransa da Jamus duk sun ki amfani gayyatar ma’aikatar harkokin wajen kasar