May 11, 2023

Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar yara akalla 17 da batan wasu da dama,

Gwamnatin jihar Sokoto dake arewa maso yammacin Nijeriya, ta tabbatar da mutuwar yara akalla 17 da batan wasu da dama, sanadiyyar kifewar wani kwale-kwale da ya yi lodi fiye da kima.
Shugaban karamar hukumar Shagari ta jihar, Aliyu Dantani ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, lamarin ya auku ne jiya Talata, bayan wani kwale-kwale, dauke da gomman fasinjoji matasa da suka fita neman itace a dajin dake kusa da su, ya kife a cikin kogin.
A cewar Aliyu Dantani, kwale-kwalen ya yi lodi fiye da kima, lamarin da ya sanya shi kifewa a tsakiyar kogin.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar yara akalla 17 da batan wasu da dama,”