Gwamnatin Jihar Borno Zata Ginawa Yan Gudun Hijira 20,000 Garuruwa 3 A Jihar.

Jaridar Leadership ta Najeria ta nakalto gwamnatin yana fadar haka a gidan gwamnatin Jihar Borno dake Abuja.
Ya kuma kara da cewa gwamnatin tarayyar ta bawa kwamitin sake tsugunar da yan gudun hijira naira billiyon 15 don wannan aikin. Zalum ya kara da cewa gwamnatin jiharsa zata bawa gidajen idan an kammalasu ne gay an gudun hijira wadanda suke son dawowa kasar. Banda haka yace hukumomi daban daban zasu taimaka masa a wannan aikin. Daga cikinsu hukumar bada agaji ta kasa NEMA zata ci gaba da aikin bada abinci da sauran agajin da yan gudun hijiran suke bukata. Sannan jami’an tsaro zasu ci gaba da bada tsaro har zuwa lokacin kammala aikin.