September 8, 2023

Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da rufe kwalejojin kiwon lafiya da ba su da rijistar aiki a jihar

Gwamnan na jihar Adamawa ya ce, daga yanzu babu wani kwalejin kiwon lafiya da za a sake bari yana gudanar da aikinsa a jihar har sai ya samu cikakkiyar kariya daga ma’aikatar lafiyar jihar.

Alhaji Ahmadu Fintiri ya ci gaba da cewa, “Daga wannan rana gwamnati ta bayar da umarnin duk wata makaranta ko kwaleji da suke da nasaba da bayar da ilimi a kan harkokin kiwon lafiya da su dakatar da ayyukansu muddin dai gwamnati ba ta tantance su ba, kamar yadda doka ta tanadar, kuma kin bin wannan umarni zai kasance babba laifi wanda kuma gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa wajen daukar mataki mai tsauri.”

Haka kuma taron ya amince da a mayar da makarantar horas da ma’aikatan jinya da ungozoma da kwalejin shari’a da suke a garin Yola karkashin kulawar ma’aikatar ilimi da ta shari’a domin dai samun cikakken kulawa tare da sanya ido.

Ha’ila yau gwamnan na jihar ta Adamawa ya bayar da umarnin dauke kwalejin fasahar kiwon lafiya dake Mubi zuwa garin Michika, inda ya yi kira ga al’ummar garin na Michika da su bayar da hadin kan da ya kamata domin bunkasuwar kwalejin

 

©Cri

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da rufe kwalejojin kiwon lafiya da ba su da rijistar aiki a jihar”