June 1, 2023

​Gwamnatin Jamus Ta Bada Sanarwan Rufe Kananan Ofisoshin Jakadancin Rasha A Kasar

 

Gwamnatin kasar Jamus ta bada sanarwan rufe kananan ofisoshin jakadancin kasar Rasha guda 4 daga cikin 5 da take da su a kasar nan da watan nuwamba mai zuwa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Jamus Christofer Burger yana fadar haka a jiya Laraba a birnin Berlin, ya kuma kara da cewa kasar Jamus ta dauki wannan matakin ne bayan da gwamnatin kasar Rasha ta takaita yawan mutanen kasar Jamus da zasu ci gaba da zama a kasar Rasha zuwa 350 kacal.

Burger ya kara da cewa a jiya ne gwamnatin Jamus ta isar da sanarwan zuwa ga ofishin jakadancin Rasha a Berlin, sannan ya kammala da cewa matakan da kasar Rasha ta dauka kan mutanen kasar Jamus ne ya sa kasar ta dauki matakin rage Rashawa a kasar don maida martani.

Kasra Rasha dai ta bayyana bacin ranta kan matakan da kasar Jamus ta dauka ta kuma sha alwashin maida martani.

Kafin haka dai gwamnatin kasar Rasha ta zargi kasar Jamus ta tallafawa kasar Ukraine da makamai daban-daban don yakar kasar Rasha a yakin da kasashen biyu suke fafatawa fiye da shekara guda da ya gabata.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Gwamnatin Jamus Ta Bada Sanarwan Rufe Kananan Ofisoshin Jakadancin Rasha A Kasar”