January 21, 2023

Gwamnatin Iran Ta Gayyaci Jakadan Koriya Ta Kudu Kan Kalaman Batancin Kasarsa Ga Iran

 

Gwamnatin Iran ta gayyaci jakadan kasar Koriya ta Kudu domin bayyana masa bacin ranta kan kalaman shugaban kasarsa na batanci kan kasarta

Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gayyaci jakadan kasar Koriya ta Kudu da ke birnin Tehran kan kalamai masu tsauri da shugaban kasarsa ya yi a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa kan kasar Iran.

Ma’aikatar ta gayyaci Yun Kang-hyeon ne jiya Laraba, don bayyana masa tsananin rashin amincewarta kan kalaman tsoma bakin shugaban kasar ta Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol game da alakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa.

A jawabinsa ga sojojin Koriya da suke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a wata ziyarar aiki da ya kai kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a yankin Tekun Fasha, Yoon ya kwatanta barazanar da Koriya ta Arewa take yi wa kasarsa da cewa tana kama da irin barazanar da Hadaddiyar Daular Larabawa take fuskanta daga Iran. Sannan ya kara da cewa Iran tana matsayin al’ummar da ta fi yin barazana ga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Gwamnatin Iran Ta Gayyaci Jakadan Koriya Ta Kudu Kan Kalaman Batancin Kasarsa Ga Iran”