November 25, 2022

Gwamnatin Bazoum ta karrama Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da lambar yabo.

 

Gamnatin Bazoum ta karrama Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da lambar yabo gabanin taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka a gobe Juma’a.

Jim kaɗan bayan isarsa kasar ta Nijar, Shugaba Mohamed Bazoum ya karrama shi yayin wasu bukukuwa biyu da aka yi a yau Alhamis.

Bayan ba shi lambar yabon, an saka wa wani titi a Yamai sunansa, sannan kuma aka ƙaddamar da wani littafi da aka fassara daga turancin Ingilishi zuwa na Faransanci game da mulkin Shugaba Buhari.

“Ina fatan wanna littafi zai zama alƙibla ga shugabannin Afirka masu zuwa kuma ya shata musu hanyar jajircewa da nagarta da kuma kishin ƙasa.

Shugabanin ƙasa da na gwamnatocin Afrika da dama ne suka suka isa Yamai babban birnin ƙasar don halartar taron na ƙungiyar African Union. Bbchausa

Yanzu haka shirye-shiryen sun kankama na tarukan ƙungiyar Tarayyar Afirka da za su gudana daga gobe Juma’a.

Shuwagabanin ƙasa da na gwamnatocin Afrika da dama ne suka riga suka isa Yamai babban birnin ƙasar, cikinsu har da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.

Jim kaɗan bayan isarsa kasar ta Nijar ta karrama shi yayin wasu bukukuwa biyu da aka yi a yau Alhamis.

Bayan ba shi lambar yabon, an saka wa wani titi a Yamai sunansa, sannan kuma aka ƙaddamar da wani littafi da aka fassara daga turancin Ingilishi zuwa na Faransanci game da mulkin Shugaba Buhari.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Gwamnatin Bazoum ta karrama Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da lambar yabo.”