December 31, 2022

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya yi afuwa ga fursunoni 46 da ke zaman gidan yari daban-daban a fadin jihar.

 

Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan afuwar, kwamishinan shari’a na jihar Barista Junaidu Attahir ya ce gwamnan ya yi wa fursunonin afuwa bisa shawarar kwamitin da aka kafa.

Attahir ya ce gwamnan yana da ikon yafewa duk wanda aka samu da laifi kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada.

Ya ce, “A karkashin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima, Gwamna yana da ikon sakin duk wanda aka kama da laifi.

“Da zarar wani ya aikata wani laifi, Gwamna yana da ikon yafe masa.”

Ya ci gaba da cewa an kafa wani kwamiti karkashin dokar jihar da zai ba Gwamnan shawara kan fursunonin da ake ganin za a yi wa gyara.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya yi afuwa ga fursunoni 46 da ke zaman gidan yari daban-daban a fadin jihar.”