June 22, 2023

Gwamnan Kano Ya Maida Barr. Muhyi Magaji Kujerarsa

Mai girma
Gwamnan Jihar Kano, ya amince da mayar da Barr. Muhyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa, PCACC, domin kammala wa’adinsa.

Ku tuna cewa gwamnatin da ta shude ta dakatar da Barr Muhyi daga mukaminsa bisa wasu dalilai.

Wannan matakin gwamnatin ta dauka tayi ne cikin bin umarnin kotu da ta bayar.

Kamar yadda Sanusi Bature Dawakin Tofa Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna ya wallafa.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Gwamnan Kano Ya Maida Barr. Muhyi Magaji Kujerarsa”