February 26, 2023

Gwamnan Borno ya yi alƙawarin bai wa ‘yan kasuwar da gobara ta shafa tallafin N1bn

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya sanar da bai wa ‘yan kasuwar da gobara ta ƙona musu shaguna, tallafin naira biliyan ɗaya.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan kafofin yaɗa labarai Isa Gusau ya fitar, ta ce ya fitar da tallafin ne domin ragewa ‘yan kasuwar raɗaɗi da suke ciki bayan ƙonewar shagunansu da kuma irin wahalhalu da za su iya shiga idan ba su samu wani tallafi ba a nan gaba.

Sanarwar ta ce za a kafa wani kwamiti don duba irin asarar da mutane suka yi da nufin taimaka musu da abin da ya kamata.

Har ila yau, gwamna Zulum ya kuma ce za a ɗauki matakai wajen ganin an kare afkuwar irin hakan a nan gaba saboda a baya an taɓa samun irin wannan gobara.

A don haka, ya yi kira ga a kwantar da hankula a yayin da gwamnati ke ƙoƙarin ganin an tallafa wa mutanen da abin ya shafa don rage musu raɗaɗi.

A jiya da daddare ne dai aka samu tashin gobarar a babbar kasuwa da ke birnin Maiduguri, inda ta yi ɓarnar da har yanzu ba a iya tantance girmar ta ba.

Ruwayar Bbc Hausa.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Gwamnan Borno ya yi alƙawarin bai wa ‘yan kasuwar da gobara ta shafa tallafin N1bn”