August 7, 2021

GWAMNA ZULUM YA SAMAR DA GIDAJE GA ‘YAN GUDUN HIJIRA

Daga Muhammad Bakir Muhammad

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya samar da gidaje kimanin Dari Uku (300) ga ‘yan gudun Hijira da suka rasa muhallinsu sakamakon rikin da yake faruwa a jihar tsahon lokaci musamman a garuruwan da ke karamar hukumar Kaga.

Farfesa Zulum da kansa ya mika takardun gidajen ga mutane wanda yake nuna hakkin mallaka, bugu da kari, Gwamnan ya gina titi wanda tsahonsa ya kai kimanin kilomita 1.8 a garin.

Gidajen da aka gina suna da daki biyu, hadi da kantin zamani a garin domin sayen abubuwan bukata na jama’ar da aka mallaka ma gidajen.

Bai tsaya iya nan ba, haka zalika ya kaddamar da makaranta da cibiyar koyar da kwamfuyuta bisa hadin gwiwar dan majalisan da ke wakiltar yankin.

Rahoto ya tabbatar da ‘yan gudun Hijiran sun nuna farin cikinsu tare da adduar sanyawar albarka ga Gwamnan.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “GWAMNA ZULUM YA SAMAR DA GIDAJE GA ‘YAN GUDUN HIJIRA”