October 20, 2021

Gwamna Zulum ya halarci taron mauludin Manzon Allah a Maiduguri

Daga Ibrahim Darussalam


Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya halarci mauludin Manzon Allah a zawiyyar Sheikh Ahmad Abulfathi dake garin Maiduguri.

Mauludin ya gudana karkashin jagorancin halifa Sheikh Ali Ahmad Abulfathi wanda ya nuna murnar sa sosai kan halartar mauludin da Gwamnan yayi.

Khalifa Ali Ahmad Abulfathi ya bayyana cewa Gwamna Zulum shine na farko a cikin jerin gwamnonin jahar Borno wanda ya halarci taron mauludi a Zawiyyar ta Sheikh Abulfathi wadda aka saba gudanarwa sama da shekaru 70.

Ga kadan daga yadda taron ya kasance:

 

 

 

 

 

 

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Gwamna Zulum ya halarci taron mauludin Manzon Allah a Maiduguri”