December 7, 2021

Gwamna Zulum ya bada kyautar Naira miliyan 5 ga sojojin da suka jikkata a yayin arangama da dakarun ISWAP

Muhammad Bakir Muhammad


Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ziyarci jami’an sojojin da suka jikkata a yayin arangama da kungiyar masu fafurukar kafa daular musulunci a kasashen yammacin Afirka ta ISWAP a yankin Rann, da ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru wacce take karkashin karamar hukumar Kala Balge ta Jihar Borno.

A yayin ziyarar da ya kai asibitin sojoji dake barikin Maimalari a Maiduguri, Gwamnan ya jajantawa sojojin da bala’in ya shafa.

A yayin ziyarar tasa, Gwamna Zulum ya umarci rabiyar kudi a tsakanin dukka sojojin da suka raunata, hada wadanda ba a arangamar kala-Balge suka raunata ba, ga wadanda suka hada mana rahoton sun shaida cewa kudin ya kai kimanin naira miliyan biyar.

Ziyarar ta gwamna Zulum ta samu rakiyar dan majalisar jiha mai waliktan Kala Balge, da kuma kwamishinan shari’a , a bangare guda kuwa akwai jami’in gwamnati, kwamishina mai kula da harkokin kananan hukumomi da masarautu. Gwamna Zulum ya jajantawa sojojin kana kuma ya jinjina musu bisa namijin kokarin da suke na kiyaye lafiya da dukiyoyin al’ummar kasa.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar soji, Birgediya Janar Onyema Nwachuku ya shaidawa manema labarai cewa ‘yan ta’addan na ISWAP sun kansance bisa motocin yaki da kuma babura a yayin da suka farmaki jami’an da aka aike yankin na Rann don gudanar da aiyukan tsaro.

Sai dai kuma jami’an na soja sun yi nasarar kashe yan ta’addan na ISWAP guda 24, kana kuma sun kwace wasu motocin yaki mallakar yan ta’addan.

Daga cikin ababen da jami’an tsaro suka kwata sun hada da; bindiga kirar AK 47 har guda 18, da makami kirar M-12 guda a tare da harsasai da dama.

A arangamar ne jami’an soja suka tilastawa yan ta’addan guduwa inda suka bar makaman su, duk da cewa jami’an tsaro har 7 sun rasa rayukan su a yayin arangamar.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Gwamna Zulum ya bada kyautar Naira miliyan 5 ga sojojin da suka jikkata a yayin arangama da dakarun ISWAP”