September 21, 2021

Gwamna Umahi: Jihohin Kudu Maso Gabas Kan Sami Duk Abin Da Suke Bukata Daga Gwamnatin Tarayya

Daga Balarabe Idriss


Gwamnan jahar Ebonyi, David Umahi ya bayyana cewa babu wani abu da al’ummar Kudu maso gabashin Najeriya zasu rasa daga gwamnatin tarayya in za su bi hanyoyin tattaunawa da fahimtar juna.

Gwamna Umahi ya bayyana hakan ne a yau Talata a garin Abakiliki, babban birnin Ebonyi, a yayin da ya kaddamar da mambobin majalisar sarakunan gargajiya na yankunan Kudu maso gabashin Najeriya wanda mai girma Eze Charles Mkpuma ya jagoranta.

A yayin gabatar da jawaban sa gwamnan ya nuna cewa rawar da sarakunan gargajiya ke takawa na da tasiri sosai wasu lokutan kan matsalolin da ake fama da su tsaro a yankin.

Gwamnan ya bayyana cewa abubuwan da ke gudana a yankin a yanzu haka ya saba da al’adun su, ya kuma bayyana cewa dole ne su tashi tsaye tsayin daka, ya ce babu wani abu da baza su iya samu ba a Najeriya ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna. Ya kara da basu shawarar kokarin bada goyon baya ga gwamnonin yankin.

Ya yaba ma sarakunan gargajiyan kan kokarin su a baya bayan nan kan ganin su na tabbatar da zaman lafiyar, inda ya siffata su da kashin bayan samar da zaman lafiya tsakanin al’ummar Igbo.

Ya bukaci sarakunan da su nemi hanyoyin ganawa da mambobin kungiyar rajin kafa kasar Biafra (IPOB) da kuma sauran kungiyoyi masu ra’ayin ballewa daga Najeriya don tattaunawa da su.

Daga karshe gwamnan ya ja kunnen masu goyon bayan kungiyar IPOB daga cikin al’ummar Igbo, inda ya bayyana cewa a yau yan wannan kungiyar sun yi hadaka da yan fashi da makamai, masu garkuwa da mutane da kuma kungiyoyin asiri, inda ya nusar da mutanen sa da su tambayi kawunan su cewa idan har gwagwarmayar kungiyar IPOB don cigaban al’ummar IPOB ne mai yasa kullum yankin Igbo ke dada fadawa cikin ibtila’o’i sanadin barnar yan kungiyar ta IPOB?

Ya bayyana cewa yan kungiyar IPOB suna cutar da al’ummar Igbo ne ta hanyar hamayyar da suke da sauran yankunan Najeriya da ke amfanar da yankin ta Kudu maso gabashin.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Gwamna Umahi: Jihohin Kudu Maso Gabas Kan Sami Duk Abin Da Suke Bukata Daga Gwamnatin Tarayya”