February 27, 2023

Gwamna Lalong ya fadi zaben Sanatan Filato ta Kudu

 

Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong na jam’iyyar APC, wanda shi ne Daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na APC, ya sha kaye a zaben Sanatan Filato ta Kudu.

AVM Napoleon Bali (mai ritaya) na jam’iyyar PDP ne, ya lashe zaben.

Dan takarar na jam’iyyar PDP Napoleon Bali, ya kayar da gwamna Lalong na jam’iyyar APC ne, banyan da ya sami kuru’u 148,844.

Gwamna Lalong, ya zo na biyu da kuru’u 91,673.

Kazalika, Lalong ya fadi Karamar Hukumarsa ta Shendam ga jam’iyyar PDP.

Daga Hussaini Isah, Jos

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Gwamna Lalong ya fadi zaben Sanatan Filato ta Kudu”