January 25, 2023

Gwamna Ganduje ya kori Muhyi Magaji

 

A karshe dai gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kori dakataccen shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado.

Tun a watan Yulin 2021 Gwamnatin jihar ta dakatar da Rimingado, jim kadan bayan ya bude bincike kan kwangilolin da ake zargin an baiwa kamfanonin da ke da alaka da iyalin gwamnan.

Wata wasika da sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji ya aikewa Rimingado, ta ce gwamnan jihar ya dogara ne da kudurin majalisar dokokin jihar a watan Yulin 2021 na tsige shi daga mukaminsa.

“Korar ta biyo bayan tanadin sashe na 6 na dokar hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta 2008 kamar yadda aka yi wa kwaskwarima.

Da aka tuntube shi domin jin ta bakinsa, Mista Rimingado ya soki matakin da gwamnan ya dauka, yana mai cewa gwamnati ta ƙi yin biyayya ga hukuncin kotun masana’antu ta kasa.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Gwamna Ganduje ya kori Muhyi Magaji”