October 12, 2021

Gwamna Ganduje ya kori Ɗan Sarauniya daga muƙaminsa

Daga Ibrahim Hamisu, Kano


Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da korar Injiniya Mu’azu Magaji Ɗan Sarauniya, daga shugabancin kwamitin kula da aikin shimfiɗa bututun iskar gas tsakanin Ajaokuta da Kaduna da Kano.
Rahotonni sun bayyana cewa, korar tasa ta biyo bayan rashin taɓuka abun a zo a gani wajen gudanar da shugabancin kwamitin.
Hakan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya fitar.
Sanarwar ta kuma buƙaci Mu’azu Magaji da ya miƙa harkokin kwamitin ga mataimakinsa Aminu Babba Dan Agundi, Sarkin Dawaki Babba.
Ta cikin sanarwar dai, gwamna Ganduje ya gode tare da yi masa fatan alheri.
Indai ba a manta ba, ko a watan Afrilun bara gwamnan ya kori Ɗan Sarauniya daga mukamin kwaminishinan ayyuka da ababen more rayuwa sakamakon kausasan kalamansa bisa mutuwar tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa marigayi Abba Kyari.
Sai dai daga bisani ya sake naɗa shi a matsayin shugaban kwamitin kula da aikin shimfida bututun Gas a watan Afrilun bana.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Gwamna Ganduje ya kori Ɗan Sarauniya daga muƙaminsa”