July 28, 2021

GWAMNA EL-RUFAI YA DAKATAR DA KOMAWA MAKARANTUN JIHAR

GWAMNA EL-RUFAI YA DAKATAR DA KOMAWA MAKARANTUN JIHAR

 

Gwamnatin jihar Kaduna  ta dakatar da buɗe makarantu a faɗin jihar ba tare da sanya ranar komawa ba.

 

Gwamna El-rufai, ne ya sanar da hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki a yau talata.

 

El Rufai ya ce gwamnatinsa ta yanke hukuncin ne sakamakon matsalolin tsaro da sassan jihar ke fama da shi.

 

Kazalika ya ce, gwamnatinsa na yin iyakar ƙoƙarinta wajen ganin ta kare ɗalibai daga hare-haren ƴan bindiga a jihar.

 

Ya ƙara da cewa an tura ƙarin jami’an tsaro jihar domin yaƙar ƴan bindiga don haka yana gargaɗin mazauna jihar su kasance masu kula.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “GWAMNA EL-RUFAI YA DAKATAR DA KOMAWA MAKARANTUN JIHAR”