May 24, 2024

Gwaman jihar Kano ya mika wa Sarki Muhammadu Sanusi II takardar fara aiki a matsayin Sarkin Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mika wa Sarki Muhammadu Sanusi II takardar fara aiki a matsayin Sarkin Kano

Gwamnan ya mika masa takardar aiki ne a wani biki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano yau Juma’a.

A jawabinsa na mika wa Sanusi takarda a ranar Juma’a, gwamnan ya ce, ba sabon sarki aka naɗa ba, “kujerarsa da ya tafi na wucin gadi ne yanzu muka dawo masa da ita.

Sanusi ya ci gaba zama sarkin Kano ne shekara hudu bayan tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta tube shi a 2020.

An tube shi a lokacin ne shekara shida da hawansa kan karagar da marigayi Sarki Ado Bayero ya bari a shekrar 2014.

A lokacin ne gwamnatin Ganduje ta kirkiro tsarin masarautu biyar a jihar, ta kuma nada Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano..

Sai dai gwamnan ya mikawa sarki Sanusi II takardar kama aiki bayan da wata kotun tarayya dake zaman ta a Kano ta dakatar da aikatar da sabuwar dokar da ta bada damar nada Muhammad Sanusi II a matsayin sarkin Kano.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Gwaman jihar Kano ya mika wa Sarki Muhammadu Sanusi II takardar fara aiki a matsayin Sarkin Kano”