October 8, 2023

Gwagwarmayar Falasdinawa Na Gab Da Yin Babbar Nasara

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas Ismail Haniyeh ya ce, gwagwarmayar Falastinawa tana gab da samun gagarumar nasara, bayan farmakin ba-zata da ta kai kan yankunan da Isra’ila ta mamaye.

Ismail Haniyeh ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a daren jiya Asabar, bayan da mayakan Falasdinawa suka kaddamar da farmaki mafi girma na yakar gwamnatin mamaya ta yahudawan sahyuniya, tare da ketare shingen shiga garuruwan da Isra’ila ta mamaye, inda aka harba daruruwan rokoki daga zirin Gaza.

“Muna gab da samun gagarumar nasara a kan makiya ” in ji Haniyeh. Ya ce: wannan yaki ne na al’umma baki daya, domin kuwa Falastinawa suna wannan gwagwarmaya ne madadin al’ummar muuslmi da sauran mabiya addinai da yahudawan sahyuniya ke tozartawa da kuma wulakanta wurarensu masu tsarki a Quds da sauran wurare.

Kuma daga wannan lokaci salon gwagwarmayar Falastinawa ya dauki sabon salo, ko dai su rayu cikin ‘yanci, ko kuma gwagwarmaya har su koma ga Allah.

 

 

©Voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Gwagwarmayar Falasdinawa Na Gab Da Yin Babbar Nasara”