March 15, 2023
Guterres : Yarjejeniyar Saudiyya Da Iran, Za Ta Samar Da Kwanciyar Hankali A Yankin

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya fitar da sanarwa cewa, kyakkyawar huldar dake tsakanin Saudiyya da Iran na da matukar muhimmanci wajen kiyaye kwanciyar hankali a yankin Gulf.
Haka kuma Mista Guteress, ya yabawa kasar Sin bisa irin kokarin da ta yi wajen ingiza yin shawarwari a tsakanin kasashen biyu.
A ranar 10 ga watan nan ne, kasashen Saudiyya da Iran suka gudanar da shawarwari a birnin Beijing, inda kasashen biyu suka cimma yarjejeniya, ta maido da huldar diplomasiyya a tsakaninsu, tare da jaddada cewa, bangarorin za su yi kokarin kiyaye ka’idojin kasa da kasa, da ma sa kaimin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.