January 28, 2024

​Guterres Ya Bukaci Kasashe Masu Bayar Da Gudunmuwa Su Cigaba Da Tallafawa UNRWA a Gaza

Wannan dai na zuwa ne bayan da da yawa daga cikin wadannan kasashe sun dakatar da tallafin da suke baiwa kungiyar saboda zargin da Isra’ila ke yi na cewa ma’aikatan hukumar na da hannu a harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.

Guterres ya ce a cikin wata sanarwa da ya fitar, “Yayin da na fahimci damuwarsu, kuma ni ma na firgita da wadannan zarge-zargen, ina kira ga gwamnatocin da suka dakatar da gudummawar da suke bayarwa da akalla tabbatar da ci gaba da ayyukan UNRWA.”

Manyan kasashe masu ba da taimako ga UNRWA a ranar Asabar sun sanar da dakatar da tallafin da suke bayarwa sakamakon zargin da Isra’ila ke yi na cewa ma’aikatan hukumar Majalisar Dinkin Duniya na da hannu a harin na ranar 7 ga watan Oktoba.

Daga cikin waɗannan ƙasashe: Amurka, Australia, Italiya, Kanada, Finland, Switzerland, Netherlands, Jamus da Birtaniya.

 

©VoH

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Guterres Ya Bukaci Kasashe Masu Bayar Da Gudunmuwa Su Cigaba Da Tallafawa UNRWA a Gaza”