May 24, 2023

Guteress, Ya Kalubalanci Gazawar Kasahen Duniya Wajen Kare Rayukan Fararen Hula

Babban sakataren MDD, Antonio Guterres, ya kalubalanci gazawar kasashen duniya wajen kare rayukan fararen hula a rikice rikicen dake faruwa a duniya.

Bayannin nasa dai ya zo ne a daidai lokacin da alkalumma suka nuna cewa adadin wadanda rikice rikice suka risa dasu da kuma illarsa ya karu da kashi 50% a tsakanin shekarar 2021 da 2022.

‘’ A gaskiya duniya na kan gazawa wajen sauke nauyin da rayata na kare fararen hula, kamar yadda dokokin jin kai na kasa da kasa suka tanada, a cewar Antonio Guteress, a gaban kwamitin tsaron MDD.

Kwamitin ya yi zamansa ne ranar Talata, bisa bukatar kasar Swiss, wacce ke shugabancin kwamitin a wannan wata domin tattauna rahoton da M. Guterres ya gabatar kan batun kare fararen hula a lokutan rikice rikice na masu dauke da makamai.

A bara kawia a cewar rahoton MDD, fararen hula 16,988 ne suka gamu da ajalinsu a rikice rikice guda 12 masu nasaba da makamai a fadin duniya, lamarin da ya karu da kashi 53% cikin dari idan aka kwatanta da shekarar 2021.

A rikicin Ukraine kawai a cewar MDD, fararen hula 7,957 ne suka mutu, sai kuma wasu 12,560 da suka jikkata, a cikin watanni 15 da suka gabata.

Sauren kasashen kuma sun hada DR Congo, Sudan, yankin Sahel, Somalia, Myanmar, Afganistan dama Haiti.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Guteress, Ya Kalubalanci Gazawar Kasahen Duniya Wajen Kare Rayukan Fararen Hula”