August 22, 2023
Guguwar iska mai karfi ta lalata wani gidan gona tare da hallaka kaji kusan dubu 12 a Najeriya

Iska da ruwan sama mai karfin gaske sun yi sanadin lalacewar wani gidan gonar kiwon kaji dake Rapomol a yankin karamar hukumar Barikin Ladi dake jihar Filato a arewa ta tsakiyar Najeriya, inda a kalla kusa kaji dubu 12 suka mutu.
Lamarin ya faru ne a daren Lahadi 21 ga wata, manyan dakuna 6 na kiwon kaji ne suka lalace, da kejin kiwo na zamani mai amfani da wutar lantarki da kuma turakun wutan lantarki da suka kareraye inda aka kiyasta asarar sama da Naira miliyan 250.
©cri