GOMA GA WATAN RAJAB: Haihuwan Imam Muhammad Jawad (AS).

Imam Muhammad Jawad shine ɗan Imam Aliyu Arrida ɗan Imam Musa Al-kazim ɗan Imam Ja’afar Sadik ɗan Imam Muhammad Al-bakir ɗan Imam Aliyu Sajjad ɗan Imam Hussain Shahed ɗan Imam Ali (Amincin Allah garesu).
Mahaifiyar sa: Kaizaran, ruwaya yazo daga Imam Hasan Al-Askari (AS) yace: “An halicce ta ne tsarkakkiya, abin tsarkakewa…”
Ana mata laƙabi da Ummul-Jawad, Ummul-Hassan, kuma ta kasance mafificiya a tsakanin matan zamanin ta”.
Haihuwar sa: An haife shi a madina/ Ranar 10 ga watan Rajab, a shekara ta 195 Hijira.
Shekarun: Shekarun sa 25.
Tsawon Imamancin sa: Shekara 17.
Shahadar sa: yayi shahada a ranar 29 ga watan zulƙida, shekara ta 220 bayan hijira, Ummul-fadl ne ta bashi guba da umurnin baffan sa Mu’utasim.
Inda aka binne shi: An binne shi a kazimiyya gefen kakan sa Imam Musa Al-kazim (Baghdad-Iraq).
Alkunyarsa: Abu Ja’afar (irin alkunyar kakan shi Imam Muhammad Bakir) domin bambancewa sai ake ce masa Abu Ja’afar Sani.
Lakabin sa: Jawad, Taqi, Murtada, Al-Qani’, Arradi, Mukhtar, Babul-Murad.
Rubutun kan zoben sa: العزة لله
Ina taya daukacin al’umma murnar wannan rana.
©Sheikh Emran Darussalam.