September 9, 2023

Girgizar kasa ta kashe fiye da mutum Dubu a Morocco

Akalla mutum 1,037 ne suka mutu sakamakon mummunar girgizar kasar da ta faru a Maroko ranar Juma’a, a cewar ma’aikatar cikin gida ta kasar.

Ta kara da cewa mutum 672 ne suka jikkata sakamakon girgizar kasar mai karfin maki 7.0 da ta kassara yankuna da dama na kasar.

Tun da farko wata sanarwa da ma’aikatar cikin gida ta kasar ta fitar da sanyin safiyar Asabar ta ce akalla mutum 296 ne suka mutum yayin da mutum 153 suka jikkata sakamakon girgizar kasar.

Girigizar kasar ta kuma lalata gine-gine yayin da mutane suka rika tserewa daga gidajensu cikin firgici.

Rahoton wucin-gadi ya nuna cewa girgizar kasar ta kashe mutum 296 a larduna da biranen al-Haouz, Marrakesh, Ouarzazate, Azilal, Chichaoua da kuma Taroudant,” in ji sanarwar, wadda ta kara da cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Girgizar kasa ta kashe fiye da mutum Dubu a Morocco”