Girgizar ƙasar Turkiyya da Syria: Sama da mutum 28,000 sun mutu

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon bala’in girgizar ƙasar da ya afka wa ƙasashen Turkiyya da Siriya ya zarta 28,000, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
To sai dai fatan samun ƙarin masu numfashi na gamuwa da cikas yayin da ake samun rahotonnin rashin zaman lafiya a wasu yankunan kudancin Turkiyya, lamarin da ke yin barazana ga masu aikin ceton kamar yadda wasu ƙungiyoyin agaji uku suka bayyana..
Ƙungiyar agaji ta ƙasar Jamus da takwararta ta ƙasar Austria sun dakatar da ayyukansu ranar Asabar, sakamakon abin da suka kira rikici tsakanin wasu ƙungiyoyi a yankin.
Wani jami’in ceto ya ce ana fargabar ƙaruwar tabarɓarewar tsaro, yayin da jigilar kayan abinci zuwa yankin ke gamuwa da cikas.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce zai yi amfani da ƙarfi wajen ladabtar da duk wanda yake ƙoƙarin karya doka.
Aƙalla gidaje 6,000 ne suka rushe a Turkiyya, lamarin da ke ɗiga ayar tambaya game gwamnatin Recep Tayyip Erdogan za ta iya yin abin da ya kamata domin kare rayuka.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana girgizar ƙasar da ‘mummunan bala’in’ da yankin ya taɓa gani cikin shekarar 100.
©BBC