February 13, 2023

Girgizan Kasa a Turkiyya da Siriya: Ayyukan ceto rayuka ya ci gaba a yayinda adadin wadanda suka rasa rayukan su ya haura 33,000

 

A kokarin da jami’an ceto rayuka ke yi a kasashen da iftila’in girgizan kasa ya shafe su sun ciro gawar wata jaririya mai kimanin watanni bakwai da haihuwa a karkashin wanu gini da ke Hatay na kudancin kasar Turkiyya, sa’o’I 139 biyo bayan girgizar kasar da aka yi.

 

A wani muhallin kuwa na daban a Hatay, an yi nasarar ceto rayuwar wata yarinya yar shekaru 12 mai suna Cudie bayan ta makale na tsahon sa’o’I 147. Gidajen yada labarai na kasar sun bayyana cewa an yi nasarar ceto rayuwar wata yarinyar yar shekaru 13 jiya Lahadi a Gaziantep.

An tabbatar da adadin mutanen da suka rayukan su akalla sama da 33,000 a kasashen Turkiyya da Siriya.

 

Kasar dai ta Siriya ta dakatar da fitar da sanarwar adadin mutanen da ta rasa tun ranar Juma’ar da ta gabata don haka adadin zai iya fin yadda rahotanni suka ambata.

Dubannin gine-gine sun rushe a yayin girgizar kasar a yayin da har yanzu ba’a tabbatar da sababin hakan ba.

 

Shugaban kasar Turkiyya Recep Toyyeb Erdogan a bayanin sa ya nuna cewa girgizar kasar bangare ne na jarrabawa da kuma kaddarar da Allah ya rubuta.  Sai dai kuma wasu hukumomi sun bayyana cewa sun samu takardun izinin kama wasu yan kwangila akalla 113 wanda ke da alaka da ginin da suka ruguje kana kuma an yi awon gaba da mutane 12 zuwa ga magarkama wadanda suka hada da yan kwangila.

Hukumar kai agaji ta Siriya ta zargi hukumomin kawo agaji na kasa-da-kasa da nuna gazawarta a bangaren kawo tallafi ga al’ummar arewacin Siriya.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Girgizan Kasa a Turkiyya da Siriya: Ayyukan ceto rayuka ya ci gaba a yayinda adadin wadanda suka rasa rayukan su ya haura 33,000”