Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

July 28, 2021

GINSHIKAN (SHIKA-SHIKAN) MUSULUNCI A WAJEN SHI’A

GINSHIKAN (SHIKA-SHIKAN) MUSULUNCI A WAJEN SHI’A

 Daga Muhammad Auwal Bauchi

Gabatarwa:

Tsawon tarihi musamman a wannan zamani na mu, dan’adam ya kan yi amfani da wasu hanyoyi ko kuma na’urori daban-daban na zamani wajen biyan bukatunsa da kuma gudanar da rayuwarsa cikin sauki kuma yadda ya ke so. Daya daga cikin irin wadannan na’urori ita ce na’ura mai kwakwalwa ko kuma kwamfuta wacce take gudanar da ayyuka masu ban mamaki kuma cikin sauri. A matsayin misali idan muka dauki aikin likitanci, za mu ga cewa a lokacin da wani likita yake neman wani bayani dangane da irin cuta da kuma tarihin cutar da wani mara lafiya da ya zo wajensa don neman magani, nan take daidai da irin bayanan da aka sanya mata, wannan na’urar za ta fito masa da wadannan bayanai don ya duba su da kuma sanin irin maganin da zai ba wa wannan mara lafiyan da sauransu. Haka nan dalibin jami’a ko kuma makaranta ta addini da sauransu, a duk lokacin da ya ke neman wani bayani na ilimi, cikin sauki wannan na’ura za ta fito masa da wadannan bayanai wadanda idan da a ce shi ne zai binciko su, to yana bukatar lokaci mai yawan gaske wajen gano su idan ma har zai iya gano su gaba dayan.

Wannan ‘yan wasu misalai ne kawai, amma hanyoyin amfani da ita cikin rayuwar mutane suna da yawan gaske. Haka lamarin ya ke dangane da wasu na’urorin da kuma hanyoyin daban-daban da dan’adam yake amfani da su wajen ciyar da rayuwarsa gaba tun farkon halittarsa har zuwa karshen duniya, kowane zamani daidai da irin ilimi da ci gaban da ya ke da shi.

To abin tambaya a nan shi ne cewa shin hankali zai yarda da cewa wannan na’urar da irin ayyukan da take gudanarwa, haka kawai ta samar da kanta ba tare da wani shiri da kokari daga wani bangare ba? Ko shin irin wannan tsari da ke cikin wannan na’urar da kuma irin yadda take gudanar da ayyukanta masu ban mamaki, ba zai zamanto babban shaida da ke tabbatar da irin kwakwalwa da kuma ilimin da wanda ya samar da ita yake da su ba?

To daga nan za mu iya samun wani dalili na gaba daya sannan wanda kuma kowa zai iya fahimtarsa kan cewa: wajibi ne irin wannan tsari ya kasance ne daga wajen wani masani kuma mai karfi da iko, sannan kuma babu yadda za a yi tushen irin wadannan ababe masu ban mamaki ya zamanto haka kawai ya samar da kansa, don kuwa kowane abu yana da nasa tushen da ya dace da shi da kuma alamun da suke tabbatar da shi.

Kamar yadda lagawu ne a yi tunanin cewa ruwan sanyi zai iya zama tushen konewar wani abu, haka nan lagawu ne a yi tunanin cewa za a iya samun wani tsararren tsari haka kawai bisa arashi, ba tare da akwai wani da ya samar da shi ba. Alkur’ani mai girma yana nuni da wannan lamarin cikin fadinsa:

(أَمْ خُلِقُوا مِنْ غَيْرِ شَيْءٍ أَمْ هُمُ الْخَالِقُونَ)

“Shin, an halitta su ne ba daga kome ba, ko kuwa su ne masu yin halitta? (Suratud Dur 52:35).

A saboda haka kowane abu da ka gani musamman abu mai muhimmanci da kuma kima yana da wasu tushe da ginshiki da ya ginu a kansa. Addinin Musulunci, a matsayinsa na addinin da ya zo don ya ‘yantar da bil’adama daga duhun zalunci zuwa ga haske na shiriya bisa irin tsare-tsare da hukumce-hukumcen da ya ke da su, ya ginu ne bisa kan wasu ginshikai ko kuma shika-shika guda biyar da wajibi ne kowane mumini ya sansu sannan kuma yayi imani da su.

Su ne kuwa:

 

Na Farko: Tauhidi:

 

Akwai kuskure cikin tunanin da wasu suke yin a na tunanin cewa Allah Madaukakin Sarki ya samar da wannan duniya sannan kuma ya bar ta haka nan kawai ba tare da damuwa da ita ba. A’a, duk wani yunkuri na wannan duniyar da kuma ci gaba da samuwarta suna karkashin iko da kuma mashi’a ta Ubangiji ne. Babu wani abin da samuwarsa mai yiyuwa ne da ci gaba da wanzuwarsa zai kasance ba tare da izini da irada ta Ubangiji ba. A saboda haka Allah Madaukakin Sarki shi ne mai samarwa da kuma ci gaba da dawwamar da abubuwan da ya samar bugu da kari kuma kan sa ido kansu.

A saboda haka mutumin da ya yi imani da girma da daukakar Allah Mahalicci sannan kuma ya tabbatar da wannan imani cikin zuciyarsa wacce take cike da kaunar Ubangiji Madaukakin Sarki, to kuwa ba zai taba jin kadaitaka da jin cewa an yi watsi da shi ba, face dai hasken Ubangiji zai ci gaba da haskaka zuciyarsa da kuma bayyanar da shi cikin dukkanin bangarori na rayuwarsa. A fili yake cewa irin wannan mutumin da ya yi imani da Allah Madaukakin Sarki zai sami kansa cikin farin ciki da kuma shaukin rayuwa wacce take cike da daukaka da kuma kamala.

Hankali dai yana tabbatar da cewa wajibi ne Allah Madaukakin Sarki ya zamanto shi kadai, ba tare da wani abokin tarayya ba wajen gudanar da wannan duniyar don ta tafi yadda ya kamata ba tare an ta samun karo da juna ba, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya ke fadi cikin Suratul Anbiya 21: 22 cewa:

( لَوْ كَانَ فِيهِمَا آلِهَةٌ إِلَّا اللَّهُ لَفَسَدَتَا)

“Da wadansu abubuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da kasa) face Allah, hakika, da su biyun sun baci “.

A hakikanin gaskiya Tauhidi (kadaita Allah) a ma’anarsa ta hakika yana tarbiyya da kuma shiryar da mutum ‘yantacce mai ingantaccen tunani da kwanciyar hankali ne, sannan kuma ba zai bar shi ya fada cikin damuwa da tsaka mai wuya, bata da sabani da bautar wani ba. Haka nan Tauhidi ya kan ba wa mutum ‘yanci da daukaka da kuma karama, sannan kuma ya taimaka masa wajen tabbatar da adalci na zamantakewa da kuma daukaka.

Daga nan za mu iya fahimtar sirrin da ke cikin fadin Manzon Allah (s.a.w.a) cewa: “Ku ce La’ilaha Illallah, ku sami babbar rabo”.

 

Na Biyu: Adalci:

 

Kamar yadda muka fahimci cewa Allah Madaukakin Sarki Shi ne Mahalicci Mai karfi da daukaka, ya arzurta bayinsa da sauran halittunSa da ni’imomi masu yawa da kuma tausayawa maras iyaka, sannan kuma shi kadai Yake, ba shi da abokin tarayya, babu wani Ubangiji in ba shi ba, ta haka ne ya ke tabbatar da adalcinsa a kan dukkanin halittu. A saboda haka ba ya bukatar ya yi zalunci – tsarki ya tabbata a gare shi daga aikata hakan – don kuwa babu wanda ya ke bukatar yin zalunci in ba mutum mai rauni ba.

Zalunci dai sakamako ne na jahilci da rauni da gasa da tsoro da rashi da kuma gazawa, Allah kuwa ya tsarkaka daga dukkanin  wadannan abubuwa. Allah Madaukakin Sarki, Masani ne sannan kuma Mai Karfi ta kowace fuska, da ba ya bukatar wani mutum ko wani abu ballantana ma ya ji tsoron cewa zai kubuce masa.

Irin bambance-bambancen da ake gani tsakanin ‘yan al’umma guda ko kuma al’ummu daban-daban, ba wani abu ba ne face sai don a sami damar gudanar da rayuwa a bisa tafarkinta da aka shimfida ta a kai, don biyan bukatar bil’adama. Allah Madaukakin Sarki yana fadin cewa:

(وَرَفَعَ بَعْضَكُمْ فَوْقَ بَعْضٍ دَرَجَاتٍ لِّيَبْلُوَكُمْ فِي مَا آتَاكُم)

“Kuma Shi ne Wanda Ya sanya ku masu maye wa juna ga kasa. Kuma Ya daukaka sashenku bisa ga sashe da darajoji: domin ya jarraba ku, a cikin abin da ya ba ku” (Suratul An’am 6:165).

A saboda haka ya rage wa mutum ya fahimci hanyar gaskiya wacce za ta kai shi zuwa ga kamala a dukkanin bangarori na rayuwarsa, don ya rayu kamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya so ya rayu cikin mutumci da ni’ima da alherori sannan kuma cikin mutumci a yayin mu’amalarsa da sauran bil’adama cikin gaskiya da kuma girmama juna, da kuma adalci da daidaito, da tsarkin zuciya da yafuwa, da dai sauran siffofi na alheri. Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

(إِنَّ اللهَ يَأْمُرُ بِالْعَدْلِ وَالإِحْسَانِ)

“Lalle Allah na yin umurni da adalci da kyautatawa” (Suratun Nahl 16:90).

Shin yayi daidai da hankali da kuma hikima a ce Allah Madaukakin Sarki ya umurci bayinsa da aikata adalci, amma shi kuma ya nesanci hakan? Tsarki ya tabbata a gare shi daga abin da suke siffantawa.

 

Zamu cigaba…

 

SHARE:
Akida One Reply to “GINSHIKAN (SHIKA-SHIKAN) MUSULUNCI A WAJEN SHI’A”
Ahlul Baiti
Ahlul Baiti

COMMENTS

One comment on “GINSHIKAN (SHIKA-SHIKAN) MUSULUNCI A WAJEN SHI’A

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *