January 25, 2024

Gidauniyar Agaji Ta Kasar Qatar Za ta Gina Gidaje 500,000 Ga Marasa Galihu A jihar Kaduna

 

Gwamnan Jihar Kaduna sanata Uba Sani yace gidauniya Qatar charity Foundation ta kasar Qatar na shirin gina gidaje 500,000 ga masu karamin karfi a karamar hukumar chikun dake jihar,

Wannan yana zuwa ne bayan wata ziyarar ganema Ido kan yadda ayyukan samar da gidajen ke gudana a sanabil a karamar hukumar chikun inda tuni aka gina gidaje guda 100 a karkashin shirin, kuma za’a ci gaba da gina sauran gidajen a wasu yankunan

Haka zalika gwamnati ta ce za’a samar da filayen noma da kiwon kaji don samar da rayuwa ingantatta ga marasa galihu dake zaune a gidajen.kuma ya bayyana jin dadinsa sosai game da yadda aikin ke gudana,

Ayyukan da Gidauniyar Charity Foundation ta yi sun hada da aikin gina gidaje masu yawa, tare da gina rijiyoyin burtsatse a kananan hukumomi daban-daban a fadin jihar don inganta samar da ruwan sha da tsaftar muhalli a yankunan karkara

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Gidauniyar Agaji Ta Kasar Qatar Za ta Gina Gidaje 500,000 Ga Marasa Galihu A jihar Kaduna”